Matatar mai ta Nigeria dake Fatakwal ta fara tace man fetur

0
63

Matatar mai ta Fatakwal, wadda take a matsayin mallakin gwamnatin tarayyar Nigeria ta fara tace danyen man fetur bayan kwashe tsawon lokaci ana zaton fara aikin matatar.

Kafin fara aikin nata an sha sanya Loka cewa zata fara tace danyen man, har karo bakwai amma fara aikin yana gagara saboda wasu dalilai da shugabannin Nigeria ne kadai suka sani.

A baya matatar ta tsara fara aikin a watan Maris, sannan ta dage zuwa Agusta, da Satumba duk a cikin shekarar 2024.

Babban kamfanin samar da man fetur da hada hadar sa a kasar nan NNPCL, ne ya sanar da fara aikin tace fetur din da matatar Fatakwal tayi.

NNPCL, ya kara da cewa wannan cigaba da aka fara samu zai taimakawa Nigeria wajen dogara da kanta ta fuskar bunkasar tattalin arziki da kuma samar da makamashi.

An fara gyaran matatar a shekarar 2021 karkashin kamfanin Maire Tecnimont SpA, bayan sanya hannu kan kwangilar dala biliyan 1.5, da gwamnatin tarayya ta amince da ita, sai dai a watan Disamba na shekarar 2023, aikin gyara matatar ya samu tangarda saboda tsaro da sauran wasu kalubalen.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here