Zulum ya raba Tirela 100 ta abinci ga mabukata a Borno

0
36

Gwamnatin jihar Borno, ta yi rabon motar Tirela 100 ta kayan abinci da shugaban Kasa Tinubu ya bayar don rabawa ga mabukata, a matsayin gudunmuwa ga Borno, sakamakon ambaliyar da akayi a jihar.

Gwamna Zulum, ya kaddamar da rabon a yau litinin inda aka fara da yankunan Gambarou da Ngala da sauran garuruwa.

Kayan hatsin da aka raba sun hadar da masara da gero da dawa, wanda aka raba ga wadanda suka fi fama da rashin abinci.

Da yake yi wa manema labarai jawabi bayan ƙaddamar da raba abincin, Zulum ya ce an zaɓi Ngala wajen fara rabon, sakamakon sai da ambaliyar ruwan da aka fuskanta ta raba garin baki ɗaya daga sauran ɓangarorin jihar na kusan wata huɗu.

Zulum ya yaba wa shugaban ƙasa Bola Tinubu da sauran hukumomin gwamnatin tarayya bisa goyon bayan da suka bawa jihar a lokacin da take neman taimako.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here