Dangote ya rage farashin litar man fetur

0
76

Matatar man fetur ta Dangote, ta sanar da rage farashin litar man fetur ga dillalan man daga naira 990, zuwa 970.

Shugaban sashin sadarwa na matatar Anthony Chiejina, ne ya sanar da hakan, yana mai cewa sun yi hakan saboda gabatowar karewar shekara, da kuma yabawa yan Nigeria da suka taimaka mafarkin samar da matatar ya zama gaskiya, tare da tallafin da gwamnatin tarayya ta basu.

Anthony Chiejina, ya kara da cewa hakan zai inganta harkokin samar da man fetur a cikin gida, sannan ya tabbatar da cewa zasu cigaba da samar da ingantaccen man.

Matatar man fetur ta Dangote, ta kuma ce zata yi duk mai yiwuwa don samar da wadataccen mai a kasar nan tare da hana fuskantar karancin sa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here