Daliban Najeriya zasu rufe filin jirgin Saman Abuja da hanyar Abuja zuwa Kaduna a yau Laraba

0
109

Kungiyar dalibai ta kasa NANS zata rufe filin jirgin Saman Abuja da babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna a yau Laraba a Fadi dashin da daliban sukeyi na ganin an janye yajin aikin da kungiyar Malam Jamion ta kasa ASUU keyi.

A ranar litinin ne daliban Jamion suka datse hanyar shiga filin jirgin Saman Murtala Muhammad Dake Lagos abinda ya janyo fasinjoji sukaita zaman jiran tsammani .

Shugaban kwamitin dalibai na kawo karshen yajin aikin kungiyar ASUU ,wato #EndASUUstrikenow Mr Olumide Ojo yace zasu karade kasar Nan da zanga zangar tasu tare da rufe manyan hanyoyi da filayen jiragen sama Dan matsawa gwamnati ta daidaita da Malam Jamion.

Saidai tuni gwamnatin Kaduna tayi gargadi ga daliban kan aniyarsu ta rufe hanyar Kaduna zuwa Abuja a yau Laraba .

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna Samuel Aruwan yace a yayinda gwamnatin Kaduna take baiwa kowa dama ya nemi hakkinsa ta hanyar data Dace Amma bazata aminta da Bada duk wata kofa da za’a iya samun matsala a bangaren tsaro ba.