Majalisar dattawa ta amince shugaban Nigeria ya sake ciyo bashin Dala biliyan 2.2

0
61

Majalisar dattawa ta amince shugaban Nigeria Bola Tinubu, ya sake ciyo bashin Dala biliyan 2.2.

Majalisar ta amince da bukatar ciyo bashin bayan gabatar mata da rahoton bibiyar bukatar ciyo bashin wanda shugaban kwamitin ciyo bashin cikin gida da ketare Aliyu Wamakko, ya yi.

Karanta karin wasu labaran:::An kama jagoran masu son kafa kasar Biafra

Adadin yayi daidai da naira triliyan 1.7, a kudin Nigeria, in akayi amfani da sauyin kowacce dala daya akan naira 800, kuma ance za’a yi amfani da kudin ne wajen cike gibin kasafin kudin shekarar 2024, na naira triliyan 9.1.

Wamakko, a lokacin gabatar da rahoton da ya bayar da damar amincewa da ciyo bashin yace za’a karbo shine daga kasashen waje.

A ranar talatar data gabata ne shugaban Nigeria Bola Tinubu, ya aikewa majalisar bukatar neman a sahalewa gwamnatin sa cin sabon bashin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here