Sarkin Musulman Nigeria yace Sarakuna Basa jin Tsoron Gwamnonin Jihohi

0
69

Mai alfarma Sarkin Musulman Nigeria, Alhaji Sa’ad Mohammad Abubakar III, yace babu kamshin gaskiya a zargin da akeyi cewa sarakunan gargajiya suna jin tsoron gwamnonin jihohin su.

Sarkin Musulman yace su sarakuna jagororin kasa ne, tun fil azal sannan suna da fahimtar yanayin da Nigeria ke ciki fiye da yanda gwamnoni suke fahimtar kasar.

Karanta karin wasu labaran:::Ma’aikatan Zamfara zasu shiga yajin aiki saboda kin fara biyan mafi karancin albashi

Jaridar Daily Trust, tace mai alfarma sarkin musulman yayi wannan tsokaci a lokacin da yake yin jawabi a wajen taron gidauniyar tunawa da Sardaunan Sokoto Ahmadu Bello, daya gudana a Abuja ranar Talata.

Bayanin Sarkin Musulman baya rasa nasaba da kalaman tsohon gwamnan jihar Nijer Babangida Aliyu, da a baya yace sarakunan Nigeria suna jin tsoron gwamnonin.

A cikin jawabin Alhaji Sa’ad Mohammad Abubakar III, yace sarakuna sun kasance masu girmama gwamnoni ne kawai saboda sun kasance masu ikon tafiyar da al’amuran al’umma, amma babu abinda zai sanya su jin tsoron su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here