Jihar Taraba ce tafi ko wacce jiha a Najeriya sayar da Iskar Gas Mai tsada – NBS

0
91

Hukumar kiddiga ta kasa NBS tace yanzu farashin Iskar Gas a Najeriya kullum Kara Hawa sama yakeyi a daidai lokacin da ake fama da matsalolin tsaro .

A rahoton hukumar ya nuna cewa a watan Yuli da ya gabata an sayar da tukunyar Gas Mai nauyin keji 5 akan kudi naira N4,397 Amma ya Karu zuwa naira N4,456.56 a watan Agusta da ya wuce .

Hukumar ta shaida cewa an samu Karin kudin Iskar Gas da kaso 1 da digo 3 cikin dari zuwa yanzu .

A sanarwar da da hukumar ta NBS ta fitar tace a duk Najeriya jihar Taraba ce tafi ko wacce jiha sayar da Iskar Gas Mai tsada ,inda ake sayar da tukunyar Gas Mai nauyin keji 5 akan kudi naira N4,925 sai jihar Adamawa Mai biye mata baya da ake sayarwa akan naira N4,920.

Sannan Kuma rahoton NBS yace jihar Katsina ce akafi sayar da Gas akan kudi mafi sauki inda ake sayar da tukunyar Gas Mai nauyin keji 5 akan naira N4 da Kobo 40 sai jihohin Ogun da Yobe sukabi bayan Katsina.