Tinubu ya ciyowa Nigeria bashin naira triliyan 50 a watanni 19

0
70

Shugaban Nigeria Bola Tinubu, ya ciyowa kasar bashin kudaden da yawan su yakai naira triliyan 50, daga farkon mulkin sa zuwa yau, tsawon awanni 19 kenan.

Zuwa yanzu bashin da ake bin gwamantin Nijeriya zai ƙaru zuwa Naira tiriliyan 138 a yayin da Shugaban Ƙasar ke neman amincewar Majalisar Dokoki domin ciyo karin bashin Naira tiriliyan 1.8.

Wannan ya nuna cewa gwamnatinsa ta ciyo bashin da ya haura Naira tiriliyan 50, wanda ya zarce rabin wanda ya tarar ana bin Kasar.

A yanzu haka bashin Naira tiriliyan 136 ake bin Nijeriya, sannan idan majalisa ta amince da buƙatar Tinubu ta karɓo bashin Dala biliyan 2.2 daga ƙasashen waje, yawan kuɗin zai ƙaru zuwa tiriliyan 138.

A ranar Talata Tinubu ya aike wa Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio da takwaransa na Majalisar Wakilai, Abbas Tajuddeen takardar neman amincewarsu da karɓo bashin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here