Masu gidajen mai sun fara rage farashi saboda rashin ciniki

0
100
Man fetur a Najeriya

Karancin masu siyan man fetur saboda tsada yasa masu gidajen mai rage farashin litar man a sannan kasar nan.

A kwanakin baya ana siyar da man akan farashin 1150, kan kowacce lita.

Sai dai a yanzu abin ba haka yake ba, saboda an hangi farashin wasu gidajen man suna siyar da shi akan 1115, wanda aka samu ragi da kusan nai 35 a duk Lita.

Haka zalika babu dogwayen layukan ababen hawa a gidajen man, kuma mutane basu fiya siyan man da yawa ba, ko da sunje sha.

Ko a kwanakin baya sai da Kungiyar dillalan man fetur tace karancin masu siyan man zai iya tilasta musu rufe gidajen mai akalla dubu 10 a fadin Nigeria.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here