Cutar amai da gudawa ta kashe mutane 25 a Sokoto

0
115

Cutar amai da gudawa da gudawa ta kashe akalla mutane 25 a kananun hukumoni 3, na jihar Sokoto, tare da kama mutane 1,160, a fadin Jihar.

Kwamishinar lafiya ta Sokoto Asabe Balarabe, ce ta bayyana hakan a ranar litinin, lokacin da take yiwa manema labarai bayani.

Kwamishinar tace a halin yanzu ana kan kulawa da masu fama da cutar su 15 a kananun hukumomin Silame da Kware.

Asabe Balarabe, tace an tabbatar da kamuwar mutanen bayan an yi musu gwaji.

Gwamnatin tace tana yin aiki da wata tawagar bawa wadanda suka kamu da cutar dauki, don dakile yaduwar cutar ta amai da gudawa.

Gwamnatin ta Sokoto, tace ta dauki hanyar dakile yaduwar cutar saboda ta hanyar bayar da umarnin siyo magunguna da rabasu kyauta ga mutanen kananun hukumomi 18 na jihar.

Asabe, tace gwamnatin Sokoto ta nuna jin dadi akan yadda aka samu fitowar mata suna zuwa ana duba su don basu kulawa akan abubuwan da ke damun su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here