Shugaban Nigeria ya sauka a kasar Brazil inda za’a yi taron G20

0
63
ECOWAS-chairman-Bola-Tinubu

Shugaban Nigeria Bola Tinubu ya sauka a birnin Rio de Janeiro na Brazil domin halartar taron kasashe 20 masu karfin tattalin arziki wanda za a gudanar a gobe Talata.

Shugaban na Nigeria ya sauka a Brazil da misalin karfe 3 na daren litinin.

Ministan harkokin wajen Brazil, Breno Costa ne ya tarbi Tinubu.

Tawagar da Tinubu ya tafi da ita Brazil sun hadar da ministan harkokin waje na Nigeria Yusuf Tuggar da Ministar Raya Al’adu da Yawo Bude Ido da Ƙirƙire-ƙirƙire, Hannatu Musawa da Ministan Kula da Dabbobi, Mukhtar Maiha da sauransu.

Bayan taron Tinubu, zai kuma gana da wasu shugabanni don kulla harkokin kasuwanci da inganta tattalin arziki.

Manufar taron ita ce lalubo hanyoyin inganta shugabanci da tattalin arziƙin ƙasashe da kuma muhalli.

Tinubu zai halarci taron ne bisa gayyatar da ƙungiyar tayi wa wakilai daga Ƙungiyar Tarayyar Afrika (AU) da Tarayyar Turai (EU).

Mambobin Kungiyar G20 sun hadar da Argentina, Australia, Brazil, Kanada, China, Jamua, Faransa, Indiya da Indonesia.

Sauran su ne Italya Japan, Koriya ta Kudu, Mexico, Rasha, Saudiyya, Afirka ta Kudu, Turkiyya, Amurka da Birtaniya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here