Nigeria zata ciyo bashin naira triliyan 9 don cike gibin kasafin shekarar 2025

0
63
Bola Ahmed Tinubu
Bola Ahmed Tinubu

Majalisar Zartaswar Najeriya tace zata ciyo bashin Naira tiriliyan 9 domin cike gibin Kasafin Kudin shekarar 2025.Ministan Kasafin Kudi da Tsare Tsaren Tattalin Arziki, Atiku Bagudu ne ya bayyana hakan yayin zantawarsa da manema labarai a birnin tarayya Abuja ranar alhamis.

Majalisar Zartarwar ta amince da kasafin kuÉ—in na 2025 da ya kai naira tiriliyan 47.9.

Da yake yi wa manema labarai jawabi bayan kammala taron majalisar da Shugaba Bola Tinubu ya jagoranta, Ministan ya ce kasafin kudin ya kunshi manyan ayyuka da kuma na musamman da za a gudanar.

Za a mika kasafin gaban majalisun dokoki na kasa domin yin nazari da kuma amincewa da shi.

A cikin kasafin za a ciyo sabon rancen da ya kai naira tiriliyan 9.2 don cike giɓin kasafin kuɗin na shekarar 2025.

Ya ce an yi hasashen samun bunƙasar yawan kayayyakin da ake samarwa a cikin gida da kashi 4.6 cikin 100.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here