Gwamnatin Kano ta zargi ma’aikatan lafiya da sace magani a asibiti

0
111
Abba Gida-Gida
Abba Gida-Gida

Gwamnatin jihar Kano, ta zargi ma’aikatan lafiya da sace magungunan da ake samarwa don rabawa mutane kyauta, inda tace ma’aikatan suna hada kai da mutanen da ake bawa maganin wajen yin satar.

Kwamishinan lafiya na jihar Dr. Abubakar Labaran Yusuf, ne ya bayyana lokacin wani taron masu ruwa da tsaki wanda cibiyar sadarwa ta CCSI, ta shirya.

Yace matsalar sace magani a asibitocin Kano itace babban kalubalen shirin bayar da maganin kyauta, ga mutanen dake da karamin karfi kuma ba zasu iya siyan maganin ba.

Yace sace maganin da ma’aikatan lafiya keyi shine yake hana cin nasarar bawa wadanda suka cancanta magani.

Sai dai kwamishinan lafiyar na Kano, yace sun kaddamar da wani tsarin yin rijistar duk wanda aka bawa maganin don sanin ainihin wadanda suka ci gajiyar shirin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here