Nuhu Ribadu yace cire tallafin man fetur ya yiwa Nigeria amfani

0
89

Mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, NSA Nuhu Ribadu ya bayyana cewa, cire tallafin man fetur da shugaban kasa Bola Tinubu ya yi amfani a Nigeria wajen kawo karshen fasa kwaurin man fetur da ake yi zuwa makwabtan kasashe.

Ribadu ya bayyana haka ne a Abuja ranar Laraba, lokacin da suka yi wani taro da shugaban Hukumar hana fasa kwauri ta Nigeria.

Yace Nigeria tana taimakawa wasu kasashen ne a lokacin da ake biyan tallafin sakamakon fasa kwaurin man da ake yi zuwa wasu kasashen.

Yace a baya jami’an custom sun sha fama da masu fasa kwaurin man fetur, amma ana samun bata garin sojojin dake taimakawa ayi fasa kwauri a baya, inda yace yanzu abin ya zama tarihi.

Ribadu, yace kowa ya zama mai siyar da fetur a Nigeria saboda biyan tallafin man.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here