An rantsar da sabon gwamnan jihar Edo a yau litinin

0
110

An rantsar da Monday Okpebholo a matsayin sabon gwamnan jihar Edo dake kudancin Nigeria.

Sanata Okpebholo wanda dan jam’iyyar APC ne ya doke abokin takarar sa na jam’iyyar PDP, Barr. Asue Ighodalo a zaben gwamnan jihar Edo da aka gudanar ranar 21 ga watan Satumba.

Karanta karin wasu labaran:::Yan ta’adda sun kone gonaki kafin girbe su a jihar Kaduna

An ranstar da shi tare da Dennis Idahosa a matsayin mataimakin gwamna.

Babban alkalin jihar Daniel Okongbowa ne ya jagoranci rantsuwar.

Sai dai tsohon gwamnan jihar Godwin Obaseki bai halarci taron rantsuwar ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here