Miji ya kone matar sa da fetur bayan samun sabani

0
65

Yan sanda sun kama Wani magidanci mai shekaru 55 Olubunmi Johnson, a Jihar Ogun, bisa zargin kone matarsa da wuta a garin Ota.

Rahotanni sun bayyana cewa ya kone matar misalin karfe 8:30 na daren ranar Juma’a, daga gabata bayan sabani ya shiga tsakanin su, a mazaunin suda ke titin Fagbuyi, Ilogbo.

Karanta karin wasu labaran:A karon farko kowanne Bitcoin daya ya kai dala dubu 80

Ana zargin Johnson da zuba wa matarsa mai suna Kikelomo fetur sannan ya cinna mata wuta.

Kakakin ‘yan sandan jihar, Omolola Odutola, ce ta tabbatar da faruwar lamarin a ranar Litinin.

Ta ce iyalan mamaciyar ne suka sanar da ‘yan sanda faruwar lamarin.

Odutola ta kara da cewa, duk da har yanzu ba a san musabbabin sabanin ba, amma an garzaya da matar asibiti.

Ta bayyana cewa an kama Johnson, kuma ‘yansanda na bincike kan lamarin a matsayin yunkurin kisa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here