Jami’an NDLEA sun hallaka dalibin makarantar Sakandire

0
76

An yi zargin cewa wasu jami’an Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA) sun yi sanadiyyar rasuwar wani dalibin makarantar sakandire a Unguwar Dangi ta Ƙaramar Hukumar Kanam da ke Jihar Filato.

Mazauna unguwar sun bayyana cewa jami’an sun kashe matashin mai suna Faisal Yakubu Hussaini lokacin da suka kai wani samame.

A cewar mutanen wadanda suka nemi bahasin ko an kai samame yankin ne saboda aikata wani laifi, jami’an sun gaza bayar da wani gamsasshen bayani.

Shugaba da kuma Sakataren Ƙungiyar Ci gaban Kanam, Barista G Abdullahi da ND Shehu Kanam, sun tabbatar da faruwar lamarin.

Mutanen sun Kuma yi Allah wadai da faruwar lamarin.

Shugabannin sun bayyana damuwa kan hakan wanda suka bayyana shi a matsayin keta iyakar ’yancin matashin da abin ya shafa.

A yayin da suke tabbatar da cewa jami’an na NDLEA suna da damar aiwatar da ayyukansu bisa duk wani tanadi da doka ta yi, sun kuma yi tir da faruwar lamarin da cewa sai an bi wa matashin hakkin sa.

Cikin sanarwar da suka fitar, sun bukaci mahukunta su gaggauta kama jami’an da ake zargi da wannan aika-aikar saboda su fuskanci hukunci.

Jaridar Aminiya ta tuntubi mai magana da yawun rundunar NDLEA, Abba Muhammad Sani, inda ya ce zai gudanar da bincike gabanin mayar da martani kan lamarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here