Gwamnan Kano ya gabatar da kasafin kudin shekarar 2025

0
70
Abba Gida-Gida
Abba Gida-Gida

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya gabatar wa majalisar dokokin jihar kasafin kudin shekarar 2025, da ya tasarwa naira biliyan 539.

Kasafin ya kunshi naira biliyan 312, na ayyukan raya kasa, sai biliyan 236, na ayyukan yau da kullum.

An warewa bangaren ilimi naira biliyan 168, a cikin kasafin wanda ya kasance kaso 31, na yawan kasafin.Gwamna Abba, yace kasafin shekarar mai kamawa zai bayar da fifiko a bangaren samar da ayyukan raya al’umma, da inganta fannin ilimi.

A nasa jawabin kakakin majalisar dokokin Kano, Ismail Falgore, ya bayyana gamsuwar sa akan yadda aka tsara kasafin, tare alkawarin amincewa da kasafin ba tare da bata lokaci ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here