Gobara ta tashi a kusa da kasuwar kantin kwari dake Kano

0
95

Gobara ta tashi a wasu kantina da ke kallon kasuwar Kantin Kwari a daren yau alhamis.

Wakilin mu da ke wajen ya rawaito cewa jami’an hukumar kashe gobara na jihar na kokarin kashe wutar a wannan lokaci.

Ana kyautata zaton na’urar din wutar sola mai amfani da rana ce tayi sanadiyyar tashin wutar.

Zuwa yanzu ba’a san adadin asarar da aka yi ba, ko kuma wadanda suka jikkata.

Muna tafe da karin bayani akan wannan labari a nan gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here