Tinubu ya dakatar da taron majalisar zartarwa saboda mutuwar shugaban sojoji

0
108

Shugaban Nigeria Bola Ahmed Tinubu, ya bayar da umarnin dage lokacin gudanar da taron majalisar zartarwa ta tarayya don nuna alhinin mutuwar babban hafsan sojojin kasar, Taoreed Lagbaja, daya mutu a daren jiya Talata yana da shekaru 56 a duniya.

Tinubu ya ce za’a sanar da wani lokacin na da ban don gudanar da taron.Lagbaja ya mutu a sakamakon rashin lafiyar da yayi fama da ita tsawon lokaci.

Kafin sanar da mutuwar Lagbaja, an shirya gabatar da taron majalisar a yau laraba.Lagbaja, ya kasance shugaban sojojin Nigeria a tsakanin 19 ga watan Yuni na shekarar 2023, zuwa 5 ga wata Nuwamba na shekarar 2024.

Mai taimakawa shugaban kasar a fannin yada labarai da tsare tsare Bayo Onanuga, ya sanar da cewa Tinubu, ya bayyana alhinin mutuwar babban hafsan sojojin, tare da yiwa iyalan sa ta’aziyyar rashin sa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here