Wutar lantarkin Nigeria ta sake lalacewa baki daya

0
89

Babban layin wutar lantarkin Nigeria ya sake lalacewa baki daya.

An samu fitar labarin lalacewar a yau Talata bayan da aka gyara wutar yan makonni da suka gabata.

A watan daya gabata an samu lalacewar babban layin wutar lantarkin Nigeria har sau uku, wanda hakan yake kawo nakasu ga harkokin kasuwanci da tattalin arzikin kasa.

Shafin gidan talbijin na Channels, ya rawaito cewa wutar ta lalace da misalin karfe 3 na rana, duk da cewa har kawo lokacin rubuta Wannan labari kamfanin rarraba lantarki na kasa TCN, bai ce komai akan lamarin ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here