Buhari ya ziyarci Borno don yin jajen ambaliyar ruwa

0
73

Tsohon Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari, ya ziyarci birnin Maiduguri na jihar Borno, domin jajanta wa al’ummar jihar kan iftila’in ambaliya da suka fuskanta a baya.

Ya kai ziyarar a yau Talata.Ambaliyar ta faru lokacin da Buhari, yake ziyara a kasar Burtaniya.

Buhari, ya samu tarba daga gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum da Sanata Ali Ndume, sannan ya ziyarci fadar Shehun Borno domin jajanta masa iftila’in.

Idan za’a iya tunawa ambaliyar ruwan da Maidugurin jihar Borno ta fuskanta sakamakon fashewar tafkin Alou, tayi sanadiyyar mutuwar mutane da yawa, da kuma asarar dukiyoyi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here