Kotu ta rushe tuhumar da ake yiwa kananun yaran da gwamnatin tarayya ta kama

0
69

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta soke tuhumar zargin cin amanar kasa da ake yi wa kananun yaran arewa da aka kama lokacin zanga-zangar yaki da yunwa su 150.

An soke tuhumar ne bayan ministan shari’a na Nigeria Prince Lateef Fagbemi, ya janye zargin da ake yi musu a madadin gwamnatin tarayya.

Alkalin kotun, Mai Shari’a Obiora Egwuatu, ya amince da bukatar janye karar tare da bayar da umarnin sakin yaran.

Shugaban Nigeria Bola Tinubu ne ya umarci dakatar da shari’ar da ake yi wa yaran tare da bayar da umarnin sakin su a ranar Litinin.

Tuni dai aka fitar da yaran daga gidan gyaran hali na Kuje, dake Abuja, don mika su ga iyayen su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here