Amurkawa sun fara kada kuri’ar zaben shugaban kasa

0
58

A yau talata 5 ga watan Nuwamba Amurkawa suka fita rumfunan zabe domin kada kuria’r da zata basu sabon shugaban kasa tsakanin tsohon shugaban kasar Donald Trump, na jami’yyar Republican da kuma mataimakiyar shugaban kasar mai ci a yanzu Kamala Harris ta Jam’yyar Democrat.

Karanta karin wasu labaran:Amurkawa miliyan 41 sun kada kuri’a a zaben shugaban kasar dake tafe a watan Nuwamba

Kafin wannan rana sama da Amurkawa dubu 70, sun kada kuri’ar su a zaben wurwuri, ta manhajar aikewa da sakonni wato email.

An fara yin zaben a yau da misalin karfe 5, agogon Amurka daidai da karfe 11, na safe agogon Nigeria, wanda aka fara zaben a yankin Vermont.

Za’a sanar da sakamakon zaben da zarar an kammala kirga yawan kuri’un da kowanne dan takara ya samu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here