Dan sandan sarauniya yayi sanadiyyar mutuwar sojan Nigeria

0
65

An samu labarin mutuwar mutum biyu a karamar hukumar Obi ta jihar Nasarawa bayan wani rikici ya faru tsakanin soja da dan sandan sa kai mai aiki a ofishin jami’an yan sanda na Jenkwe.

Lamarin ya faru a ranar lahadi data gabata.A wata sanarwa da kakakin rundunar yan sandan jihar, DSP Rahman Nansel ya fitar ya ce rikicin ya biyo bayan sace wani babur da aka yi.

Sanarwar ta ce, bayan an kai rahoton satar babur din, yan sanda sun kama wanda ake zargi tare da taimakon wani jami’in sandan sarauniya wanda aka fi sani da constable da ke aiki a ofishin.

A lokacin da aka kama wanda ake zargi da satar ne wani soja wanda ke aiki a jihar Borno, ya zo hutu, ya tare yan sanda domin hana su tafiya da wanda ake zargin.

Ana tsaka da hakan aka fi karfin sojan, sannan rikici ya barke, har daga baya sojan ya rasu.Sanarwar ta kara da cewa daga baya wasu matasa sun zo sun kone ofishin yan sandan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here