Uwar gidan shugaban Nigeria zata jagoranci yiwa kasar adduar saukin rayuwa

0
32

 Uwargidan shugaban Nigeria Sanata Oluremi Tinubu da mai bawa shugaban kasar shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu za su jagoranci addu’a ta musamman domin neman saukin matsalolin da Najeriya ta tsunduna.

Addu’ar zata gudana ne bisa jagorancin jagororin addinin Musulunci da Kirista, domin neman taimakon Allah a kan kalubalen da kasar ke ciki.

Chief Segun Balogun Afolorunikan, wanda shi ne darakta-janar na shirya addu’ar shine ya sanar da hakan a Abuja.

Ya ce akwai bukatar kowa ya bayar da gudunmuwar sa don ganin an magance matsalar da Nigeria ke fuskanta.

Yan Nigeria dai sun afka cikin kuncin rayuwa bayan da shugaban Kasa Tinubu ya cire tallafin man fetur.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here