Shin Aliyu Sani Madakin Gini, ya shirya ficewa daga jam’iyyar NNPP ne

0
95

A yammacin jiya lahadi ne aka samu fitar labarin cewa dan majalisar wakilai na mazabar Dala a kwaryar birnin Kano, Aliyu Sani Madakin Gini, ya kalubalanci mai gidan sa na siyasa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.

Sanata Kwankwaso shine jagoran jam’iyyar NNPP a matakin Nigeria baki daya.

An samu bazuwar bayanan Ali, da yake caccakar Kwankwaso, har ma yana neman gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya tsaya da kafar sa, ma’ana ya dena yiwa Kwankwaso biyayya.

Tun a baya dai ake ganin fara samun takun saka tsakanin Kwankwaso da Ali Madaki.

Kafin yanzu ana ganin Ali Sani Madakin Gini, matsayin na hannun daman Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.

Ali yana da hujjar cewa ana aiwatar da wasu abubuwan da basu dace ba a tafiyar kwankwasiyya.

Tuni Ali ya cire jar hula , wadda ita ce ke nuna alamun yiwa Kwankwaso biyayya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here