Mutane miliyan 33 na cikin barazanar fuskantar karancin abinci a Nigeria 

0
61

Wani rahoton bincike daga Cibiyar Cadre Harmonisé (CH) ya bayyana cewa akwai barazanar karancin abinci mai tsanani da ke tunkarar Nijeriya, inda aka ƙiyasta cewa kimanin mutane miliyan 33 da dubu dari 1 za su fuskanci matsanancin rashin abinci da abinci mai gina jiki daga yanzu zuwa tsakiyar shekarar 2025.

Wannan bincike, wanda gwamnatin Nijeriya ta gudanar tare da haɗin gwuiwar hukumar abinci da aikin gona ta majalisar ɗinkin duniya (FAO), ya nuna cewa zuwa Disamba 2024, akwai hasashen mutane miliyan 25, musamman a Arewa maso Gabas da Arewa ta Tsakiya, za su shiga matsanancin karancin abinci.

Rahoton ya bayyana rashin tsaro, da hauhawar farashi, da matsalolin yanayi, da kuma talauci mai tsanani a matsayin manyan abubuwan da ke haifar da karuwar wannan matsala.

Wakilin hukumar samar da abinci ta Majalisar dinkin duniya, a Nigeria Kouacou Dominique Koffy, tare da jami’an gwamnatin Nijeriya, sun yi kira da a ɗauki matakan gaggawa, kamar bayar da tallafin abinci, shirye-shiryen ƙarfafa juriya, da taimako ga gidajen da ke cikin mawuyacin hali domin daƙile mummunar matsalar da ke tunkara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here