Sabon rikici ya kunno kai tsakanin Dangote da dillalan man fetur

0
67

An samu sabon rashin fahimta tsakanin dillalan mai da Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, kan zargin da ya yi musu ma kin sayen man fetur daga matatar sa.

Dangote ya bayyana cewa matatar na da lita 500,000 na man a kasa, wanda zai ishi Nigeria tsawon kwana 12.

Amma ’yan kasuwa sun ce dole sai ya sayar musu da man akan farashi mai sauki, saboda man nasa ya yi tsada.

Tun da Matatar Dangote ta fara tace man fetur ake samun taƙaddama tsakanin kamfanin da jami’an gwamnati da kuma ’yan kasuwa.

Yan kasa sun yi fatan cewa fara aikin katafariyar matatar zai samar da isasshen mai da kuma saukin sa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here