Gwamnan Rivers ya daukaka kara akan hana bashi kudi daga gwamnatin tarayya

0
64

Gwamnatin jihar Rivers ta daukaka kara kan hukuncin babbar kotun tarayya da ya hana babban bankin kasa CBN bai wa jihar kason kudin ta daga asusun gwamnatin tarayya.

A ranar Laraba kotun, Mai Shari’a, Joyce Abdulmalik ya yanke hukuncin.

Mai shari’a Abdulmalik ya ce kason jihar da Gwamna Fubara ke karba daga gwamnatin tarayya tun daga watan Janairu zuwa yanzu ya sabawa ka’ida, kuma dole a dakatar.

Alkalin ya ce gabatar da kasafin kudin da gwamna Fubara ya yi a gaban yan majalisar jihar guda hudu ya sada da kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999.

Bayan haka ne kwamishinan yada labaran jihar, Joseph Johnson, ya shaida wa Jaridar Punch cewa gwamnatin jihar ta daukaka kara kan batun, tare da fatan cewa kotun daukaka kara zata dakatar da hukuncin babbar kotun tarayyar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here