Gwamnatin tarayya tace Sai 12 ga Nuwamba za’a samu wuta a jihohin Arewa 17

0
80
wutar lantarki

Gwamnatin tarayya ta tabbatar da kokarin da take yi na ganin cewa an gyara wutar lantarkin arewa a cikin kankanin lokaci.

An samu bayanin hakan bayan da ministan lantarki Adebayo Adelabu, yace za’a kammala daukacin gyara wutar jihohin arewa 17 nan da kwanaki 13, wato a ranar 12 ga watan Nuwamba.

Hakan ya nuna cewa jihohin Arewa 17 zasu cigaba da zama a cikin duhu har zuwa 12 ga Nuwamba.

Adelabu, yana yin wannan bayani a lokacin da yake jawabi ga majalisar wakilai inda yace za’a yi kwarya kwaryar gyaran wutar nan da kwanaki uku.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here