Dangote ya gana da shugaban Kasa Tinubu akan siyar masa danyen man fetur

0
71

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya tattauna da kwamitin da ke yin aiki akan sayar da danyen mai da man fetur da takardar kudi ta Naira.

Ministan Kudi, Wale Edun ne, ya jagoranci kwamitin zuwa Fadar Shugaban kasa a yau Talata.

Wadanda suka halarta taron sun hadar da Alhaji Aliko Dangote, Shugaban Kamfanin Man Fetur na kasa NNPCL Mele Kyari, Shugaban Hukumar tattara Haraji (FIRS), Zacch Adedeji da kuma Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Yemi Cardoso.

Sauran mutanen da suka halarci taron sun hada da Malam Farouk Ahmed daga Hukumar Kula da albarkatun Man Fetur (NMDPRA) da kuma Gbenga Komolafe daga Hukumar Kula da Ma’adanan Mai.

Bayan ganawar, ministan kudin ya shaida wa manema labarai cewa sun tattauna kan shirin sayar da danyen mai ga matatun mai na cikin gida ta hanyar yin amfani da Naira sabanin dalar Amurka.

Ya bayyana cewa wannan shirin na shugaban kasa Tinubu yazo sakamakon zuba jari mai yawa da Dangote ya yi a matatarsa.

Wale, ya kara da cewa dukkanin masu ruwa da tsaki a fannin mai sun dauki alkawarin ganin shirin ya samu nasara tare da magance duk wata matsala da ka iya tasowa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here