Sojojin Nigeria sun kashe mayakan Boko Haram a Borno

0
80
Sojin sama

Rundunar sojin saman kasar nan ta ce jiragen samanta sun kashe mayakan Boko Haram masu yawa a ranar 25 ga Oktoba a garin Bula Marwa dake jihar Borno.

Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Air Comodore, Olusola Akinboyewa ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin a birnin tarayya Abuja.

Akinboyewa ya ce sun gano cewa Bula Marwa ne garin da mayakan Boko Haram suke taruwa, inda suka hango babura suna zirga zirga, hakan ya sa aka tura jiragen sama yankin, don fatattakar mayakan kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya ruwaito.

Yace hotunan da jirgin ya dauka daga sama sun tabbatar da cewa wadannan mutane yan Boko Haram ne, tare da babura guda 12.

Da ganin haka jiragen suka bude wuta, bayan haka ne wasu mayakan suka zo kwashe yan uwansu da aka raunata, inda aka sake budewa wadanda suka zo wuta tare da kashe su.

Akinboyewa ya ce an sake ganin wasu tarin yan Boko Haram sun taru a karkashin wata bishiya, inda nan ma jiragen suka kara bin su, suka yi musu barin wuta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here