Hakimai da dagatai sun yi murabus saboda shiga siyasa a Sokoto

0
78

Wasu hakimai da dagattai 19 sun yi murabus a Karama Hukumar Sabon Birni da ke Jihar Sakkwato domin shiga siyasa.

Yankunan da sarakansu suka yi murabus su ne Sabon Birnin Gabas da Tsilba da Sabon Garin Danbaki da kuma Magajin Dawaki da Dan Faru da Zumbuli da Dawakin da Kanwuri da Hande da Sabon Fegi, Tudun Dankusu da Alhazzai da sauransu, inda suka bayyana goyon bayansu ga Sanata Ibrahim Lamido.

Karanta karin wasu labaran:Gwamnatin Sokoto zata siyar da abinci a farashi mai sauki

Sun yi murabus daga sarauta mako biyu bayan Hakimin Sabon Birni, Alhaji Abdullahi Muhammad Bawa, ya sauka daga sarautarsa a a ranar 16 ga watan Oktoba, 2024.

Yace yayi hakan domin goyon bayan tafiyar siyasar Sanata Ibrahim Lamido.

Daya daga cikin wadanda suka ajiye sarautar, Dagacin Taka-Tsaba Alhaji Lauwali Shuaibu, ya shaida wa manema labarai sun mika takardu na sauka daga sarauta, amma babu wanda ya kira su don jin korafin su.

Ya ce sun dauki matakin ne bisa la’aikari da yadda Sanata Lamido ya jajirce wajen kula da jin dadinsu da kuma zuwa ya kawo dauki a duk lokacin da ’yan ta’adda suka kawo musu hari.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here