Gwamnonin Arewa sun shirya taron nemawa yankin mafita

0
77

Kungiyar Gwamnonin Arewa, ta shirya taron duba matsalolin yankin a jihar Kaduna.

Kungiyar karkashin jagorancin gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa, ta shirya taron ne don tattauna matsalolin da suka dabaibaye yankin da manufar nemo mafita.

Karanta karin wasu labaran:Sanatocin Arewa sun nemi a gaggauta gyara wutar lantarkin yankin

Taron, wanda da ake gudanarwa na tsawon kwanaki biyu ya samu halartar sarakunan yankin, bisa jagorancin Mai alfarma sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad III, da babban hafsan tsaron kasa Janar C.G Musa da sauran su.

A jawabin, gwamnan na Gombe, yayi jaje zuwa ga wadanda ambaliyar Maiduguri ta shafa, da sauran jihohin arewa, da kuma wadanda fashewar tanka a Jigawa ta shafa, da mutanen da rashin tsaro ya shafa ta hanyoyi daban-daban.

Yace manyan matsalolin da arewa ke fuskanta a yanzu su ne rashin tsaro da garkuwa da mutane da rikicin manoma da makiyaya da ta’ammuli da miyagun kwayoyi da matsalar almajiri da talauci da rashin aikin yi da karuwar yaran da ba sa zuwa makaranta.

Yace hadin kai ne zai magance wadannan matsalolin.

Gwamnan Gombe ya kara da cewa zanga-zangar matsin rayuwa da aka yi a watan Agusta ta zama wata manuniyar daukar mataki ga dukkan jagororin arewa. 

Kungiyar Gwamnonin Arewa tace dole a fitar da hanyoyin rage talauci da samar da aikin yi da sauran abubuwa a yankin.

Gwamna Yahaya yace tabbas ana yin rayuwa cikin matsin tattalin arziki musamman a yankin Arewa, don haka dole su yi wani abu cikin gaggawa.

Ya ce arewacin Najeriya na da kasar noma, wanda a cewarsa idan aka habaka, zai rage talauci da habbaka tattalin arzikin yankin.

Wanda yace Idan ana son samun nasara, dole a tallafawa manoma sannan a samar da dabarun noma na zamani, da tabbatar da tsaro a yankin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here