Makarantun Firamare zasu koma karkashin kulawar gwamnatin tarayya

0
125

Majalisar dattawa tana duba wani kudiri akan dubban yaran da ba sa zuwa makaranta a sassan Nigeria da nufin gano matsalolin da ke hana su zuwa makaranta, tare da magance su.

Karanta karin wasu labaran:Wasu fursunonin sun kammala karatun digiri a gidan gyaran hali 

Majalisar tana kuma duba yiwuwar fito da wani tsari na bai daya da zai mayar da makarantun firamare da sakandare karkashin kulawar gwamnatin tarayya, tare da ware masu kasafin kudi na musamman.

Sanata Lawal Adamu Usman, mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, kuma shugaban kwamitin ilimi a matakin farko na majalisar dattawan ne ya bayyana wa BBC haka.

Lamarin karatu a makarantun Firamare da sakandiren gwamnati a Nigeria yana cikin wani hali mara dadi sakamakon cewa gwamnatocin jihohi basu fiya basu muhimmanci ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here