Farashin fetur ya karye a kasuwar duniya

0
77

Farashin danyen man fetur ya yi sauki a kasuwannin duniya bayan da Isara’ila ta mayar da martanin hare hare zuwa Iran ranar Asabar.

Kafin yanzu an samu hauhawar farashin man saboda fargabar da ake ciki cewa Isra’ila za ta iya kai hari zuwa wajen samar da man fetur na Iran.

Karanta karin wasu labaran:Isra’ila ta kaiwa Iran hari

Sai dai kuma bayan harin farashin man ya sauka da kashi hudu cikin dari, saboda ba’a kai harin zuwa inda Iran ke samar da fetur ba.

Tun da farko, Iran, ta yi alkawarin mayar da wani martanin zuwa sansanin soji da cibiyoyin samar da makamai na Isra’ila.

An cigaba da samun rashin jituwa tsakanin kasashen biyu bayan Isra’ila ta kashe shugaban Hezbollah, Hassan Nasrallah, wanda tun a lokacin Isra’ila ta kuduri aniyar mayar da martani.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here