Ma’aikatan jami’o’in Nigeria sun fara yajin aiki

0
101

Ƙungiyoyin ma’aikatan jami’o’i da ba malamai ba sun sanar da fara yajin aiki na sai baba-ta-gani daga yau Litinin, 28 ga watan Oktoba, saboda rashin biyansu albashi na tsawon watanni hutu.

An rike wa ma’aikatan albashin nasu tun shekarar 2022.

Karanta karin wasu labaran:Me ya sa jami’o’in Najeriya suka tsuga kuɗin makaranta?

Kwamitin hadin gwuiwa na kungiyoyin NASU da SSANU, ne ya fitar da sanarwar fara yajin aikin a yammacin jiya lahadi.

Sanarwar da shugaban SSANU, Mohammed Ibrahim, da Sakataren NASU, Peters Adeyemi, suka sanyawa hannu, ta bayyana cewa duk da gargadi da zanga-zangar neman biyansu albashi, gwamnati bata dauki wani matakin hana su shiga yajin aikin ba.

Kungiyoyin tun a jiya sun umarci dukkan mambobinsu dake jami’o’in kasar nan da su gudanar da tarukan majalisarsu ba tare da wani sassauci ba.

Ana ganin hakan zai kawo tangarda ga al’amuran tafiyar da jami’o’in.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here