Kotu ta dage sauraron shariar wadanda ake zargi da kashe Sheik Aisami

0
108

Babbar Kotun jihar Yobe Dake zamanta a birnin Damaturu ta dage cigaba da sauraron shariar wandada ake zargi da kashe Sheik Goni Aisami zuwa wata Rana da ba’a ambata ba.

Mai shari’a Amina Shehu wacce ta fara hutu ,tunda farko Babban lauyan gwamnati Kuma kwamishinan sharia na jihar Yobe Barista Saleh Samanja ya nemi Kotun data Basu ishashen lokacin da zasuyi nazari akan shari’ar.

Jaridar Hausa 24 ta gano cewa an fara sauraren shariar sojojin da ake zargi su biyu da kusan Sheikh Goni a yau litinin 19 ga watan Satimba na 2022.

Mai shariar Amina tayi alkawarin cewa za’a sanar da ko wanne Bangare ranar da za’a Koma cigaba da sauraron shariar.

A ranar 27 ga watan Agusta da ya gabatar ne Rundunar Sojojin Nijeriya ta bayyana É—aukar matakin korar sojojin nata guda biyu bisa samun su da laifin kashe malamin addinin Musulunci, Sheikh Goni Aisami Gashuwa, a jihar Yobe.

Sojojin da lamarin ya shafa su ne Lance Kofur John Gabriel da Lance Kofur Adamu Gideon.

An gabatar da tsaffin sojojin ne bisa tsautsauran matakan tsaro .