Hukumar kwallon kafar Afrika taci kasar Libya tarar Dala dubu 50 saboda Nigeria

0
155

Kwamitin ladabtarwa na Hukumar kwallon kafa ta nahiyar Africa, yaci kasar Libya tarar Dala dubu 50, sakamakon abinda ya faru ga tawagar kwallon kafa ta Nigeria Super Eagles, yayin da suka halarci kasar don buga wasan neman gurbin shiga gasar cin kafin Africa wato nation Cup.

Mahukuntan Libya sun sauya wajen da aka tsara jirgin saman yan kwallon Nigeria zai sauka, tare da kin bawa yan wasan kulawa, har suka shiga wani mawuyacin hali, hakan yasa tawagar Super Eagles ta yi fushi tare da kin buga wasan suka dawo Nigeria.

A hukuncin an bawa Nigeria nasara a wasan da ba’a buga ba, da cin kwallaye 3

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here