Isra’ila ta kaiwa Iran hari

0
79

Isra’ila ta kai hare hare kan wasu wuraren aikin soja na Iran, a matsayin martani ga abin da ta kira ci gaba da kai hare hare kan Isra’ila da Iran da kawayenta ke yi.

Kakakin sojin Isra’ila Daniel Hagari, ya ce harin ragmuwar  tamkar wani nauyi ne da ya rataya a kan Isra’ila biyo bayan harba makami mai linzami kusan dari biyu da Iran ta yi a makonni uku da suka wuce.

Kamfanin dillancin labarai na Iqna ya ce an kai hari kan wasu sansanonin soji a yamma da kudu maso yammacin Tehran babban birnin kasar Iran.

Wakilin BBC a birnin Kudus ya ce Isra’ila ta takaita hare haren akan wuraren soji kadai kuma ba ta kai hari kan tashoshin nukiliya ko matatun man fetur na Iran ba.

An kuma bayar da rahoton tashin bama bamai a Damascus babban birnin kasar Syria.

Fadar gwamnatin Amurka ta White House ta ce babu hannun ta a cikin lamarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here