Mun bankado shirin da jam’iyyar APC ke yi na sayen katin zabe daga hannun al’umma – NNPP

0
120

Jam’iyyar NNPP a Jihar Kano ta ce, ta bankado wani shiri da jam’iyyar APC mai mulki ke yi na saye katin zaben daga hannun al’umma.

Jam’iyyar ta bayyana hakan ne, a yayin wani taron karawa juna sani da jam’iyyar NNPPn ta gudanar a Kano, karkashin jagorancin Garba Diso da sakataren jam’iyyar Dakta Hamisu Sadi Ali.

Jam’iyyar ta kuma zargi gwamnati mai ci a yanzu, da mayar da harkokin siyasa tamkar gado.

A don haka jam’iyyar ta bukaci hukumar zabe mai zaman kanta ta dauki matakin da ya dace kan lamarin don yiwa tufkar hanci.