An kama babban dan ta’adda a jihar Kano

0
97

Jami’an rundunar tsaron al’umma  ta Civil Defence sun kama wani da ake zargin babban dan bindiga, ne mai suna Umar Ibrahim, wanda aka fi sani da Danlami Tela, a Jihar Kano.

Kakakin hukumar, SC Ibrahim Idris Abdullahi, ya bayyana cewa an kama wanda ake zargin mai shekaru 45 a jiya Alhamis a unguwar Hotoro Yandodo da ke karamar hukumar Nassarawa.

Karanta karin wasu labaran:Shugaban kasa ya nemi jami’an tsaro su gaggauta kawo karshen ta’addanci a arewa

Bincike ya nuna cewa Ibrahim, dan asalin garin Dikke ne a karamar hukumar Funtua ta jihar Katsina, kuma yana da alaka da wani babban dan bindiga da ke da hannu wajen garkuwa da mutane da aikata ta’addanci a Funtua da kewaye.

Abubuwan da aka samu a hannun sa sun hada da waya sai layin waya guda uku, da katin cirar kudi na bankin Unity.

NSCDC reshen Kano, karkashin jagorancin kwamandan ta Mohammed Lawal Falala, ta mika Ibrahim ga sansanin Sojin saman Nijeriya da ke Funtua domin ci gaba da bincike.

Hakan na cikin matakan hukumar NCDC don hana shigowar ‘yan bindiga Kano, bayan kwanan nan ta gudanar da bincike kan maboyar yan ta’adda a Katsina, da Kaduna, da kuma Zamfara.

Hukumar ta sake tabbatar da aniyarta ta tabbatar da doka, inda ta bayyana nasarar kama ‘yan fashi 9 da wasu bata gari 45 a Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here