Shugaba Tinubu ya rushe ma’aikatun tarayya biyu

0
99
Bola Ahmed Tinubu
Bola Ahmed Tinubu

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya rushe ma’aikatun tarayya biyu.

Ma’aikatun da abin ya shafa su ne hukumara kula da yankin Neja Delta da ta wasanni.

Karanta karin wasu labaran:Gwamnatin tarayya zata hukunta jihohin da basu yi zaben kananun hukumomi ba

Bayanin hakan na cikin wata da mai taimakawa shugaban kasa akan harkokin yada labarai Bayo Onanuga ya fitar.

Shugaban ya yanke wannan hukunci a yau laraba, lokacin zaman majalisar zartarwa ta tarayya.

Zuwa yanzu shugaban yace hukumar wasanni zata cigaba ayyukan ma’aikatar wasanni.

Haka zalika an rushe hukumar kula da yankin Neja Delta, da aka mayar da ayyukanta karkashin ma’aikatar kula da cigaban shiyyoyin kasa baki daya.

Har ila yau an hade ma’aikatar yawon bude idanu da ma’aikatar al’adu.

Tinubu ya kuma rantsar da Dr Abdullahi Usman Bello, a matsayin sabon shugaban hukumar kula da da’ar ma’aikata ta kasa CCB.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here