Babbar mai shari’ar jihar Kano ta yiwa fursunoni afuwa

0
57

Babbar mai shari’a ta  jihar Kano Dije Abdu-Aboki ta yi umarnin sakin fursunoni 37 daga gidan gyaran hali na Goron Dutse don rage cunkoson da gidajen yarin jihar.

Umarnin sakin na cikin wata sanarwa da kakakin hukumar kula da gidajen yari na jihar Kano Musbahu Kofar Nasarawa ya fitar a jiya Litinin, inda ya ce an tantance fursunonin da za’a saki karkashin  umarnin babbar mai shari’ar.

A cewar Musbahu Kofar-Nasarawa, galibin fursunonin an sallame su daga gidajen yarin sakamakon yanayi na lafiyarsu ko kuma wadanda suka jima a tsare ba tare da yi musu shari’a ba.

Rahotanni sun ce mai shari’a Dije Aboki ta kuma bayar da kyautar Naira dubu 10 ga kowanne Fursuna da aka fitar daga gidan gyaran halin.

Shugaban hukumar kula da gidajen yarin jihar Kano Ado Inuwa ya yaba da matakin mai shari’ar wanda ya bayyana a matsayin kyakkyawan aiki da zai taimaka wajen rage laifuka a jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here