Gwamnan Kano ya taya Kwankwaso murnar cika shekaru 68 a duniya

0
67

Gwamnan jihar Kano, Abba Yusuf ya taya jagoran jam’iyyar NNPP na kasa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso murnar cika shekara 68 da haihuwa.

An haifi Kwankwaso a ranar 21 ga watan Satumba na shekarar 1956.

Karanta karin wasu labaran:Kwankwaso yace ba zai yi magana akan rikicin NNPP ba

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Gwamna Yusuf ya yaba da tasirin siyasar Kwankwaso da kuma gudummawar da yake bayarwa wajen ci gaban kasa, inda ya bayyana shi a matsayin jagora kuma jigo a fagen siyasar Nijeriya.

Da yake magana kan alakarsa da Kwankwaso, Yusuf ya bayyana irin dimbin ilimi da gogewa da ya samu daga aiki da Kwankwaso cikin shekaru 38 da suka gabata.

A madadin iyalai da al’ummar jihar Kano, Gwamna Yusuf ya yi wa tsohon gwamnan jihar Kano fatan alheri da samum nasara a acikin yi wa kasa hidima, da rayuwar sa ta nan gaba

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here