Ba ma’aikacinmu dake karbar albashin naira miliyan 3 kowanne wata – PenCom

0
88

Hukumar dake kula da kudaden fanshon ‘yan Najeriya da ake kira PenCom tayi watsi da rahotan dake bayyana cewar kowanne ma’aikacin ta na karbar naira miliyan 3 kowanne wata a matsayin albashi.

Hakan dai ya biyo bayan binciken da kwamitin kudi na majalisar wakilan keyi, wanda ya bukaci bayani akan yadda Hukumar ke biyan kowanne ma’aikaci naira miliyan 2 da dubu 400 kowannne wata a matsayin albashi, kamar yadda takardun da Hukumar ta gabatar musu ya nuna.

‘Yan majalisar sun bayyana matukar bacin ransu da yadda ma’aikata a Hukumar zasu dinga karbar wadannan makudan kudade a matsayin albashi, yayin da wasu ma’aikatan da suka aje aikin su ke mutuwa ba tare da sun karbi kudaden fanshon su ba.

Shugabar Hukumar ta PenCom Aisha Dahir Umar ta kasa yiwa ‘yan majalisun gamsassun bayanai, abinda ya sa kwamitin ya baiwa Hukumar umurnin komawa domin kawo cikakkun bayanai akan albashin ma’aikata 500 dake aiki tare da ita.