Sanata Kawu Sumaila ya bayar da tallafi a makarantu da asibitocin Kano ta kudu

0
82

Sanata Kawu Sumaila ya bayar da tallafin Kujerun Makaranta Sama da 3,000 da gadon kwanciyar marasa lafiya a asibiti guda 1,000.

Sanata Suleiman Abdurrahman Kawu Sumaila mai wakiltar Kano ta Kudu ya aiwatar da wannan babban kokarin daga darajar mazabarsa inda ya bayar da tallafin kujeru da teburan karatu sama da dubu uku da gadon kwanciyar marasa lafiya a asibiti har guda1000 da katifu.

An gudanar da  taron bayar da tallafin a unguwar Tokarawa a ranar lahadi data 20 ga watan Oktoba, 2024, wanda hakan ya tabbatar da manufar sa ta son magance matsalar karancin ilimi da kiwon lafiya a yankin Kano ta Kudu.

Karanta karin wasu labaran:Gwamnan Kano ya mikawa Sarkin Gaya Sandar Mulki

Gudunmawar, wacce ta kasance wani bangare na shirye-shiryen samar da ayyukan cigaban mazabar Kano ta Kudu, Sanata Sumaila, yana da nufin habaka cibiyoyin ilimi da ayyukan kiwon lafiya a yankin. 

Sanata Sumaila, yace manufar bayar da tallafin itace a samar da ingantaccen yanayin koyo ga dalibai da kuma inganta kula da marasa lafiya a fadin Kano ta Kudu.

Ya kuma jaddada cewa, wannan shi ne mafarin kokarinsa na kawo sauyi ga muhimman sassan lafiya da Ilimi a mazabar tasa.

Sanata Kawu Sumaila ya kara da cewa a  matsayi sa na wakili aikin sa ne tabbatar da cewa makarantun yankin da asibitoci sun samu abubuwan da suke bukata wajen gudanar da aiki ba tare da tangarda ba. 

Haka zalika ya roki wadanda aka bawa tallafin suyi amfani da shi ta kyakyawar hanyar da al’ummar Kano ta kudu zasu cigaba da cin moriyar kayan.

Gwamna Abba Kabir Yusuf, wanda ya halarci taron, ya yabawa kokarin da Sanata Kawu Sumaila ke yi, inda ya bayyana cewa irin wannan gudumawa na da matukar muhimmanci ga ci gaban jihar Kano baki daya. 

Gwamna Abba yace ana kyautata zaton wannan tallafi zai inganta harkokin ilimi da kiwon lafiya, musamman rage yawan mata masu juna biyu da suke rasa ransu lokacin haihuwa a fadin Jihar Kano.

Sanata Kawu Sumaila ya kuma bayar da tallafin karatu ga dalibai sama da 600, masu karatun bangaren kimiyya, da nufin tallafa wa iliminsu da kuma gudunmawar da za su bayar a fannin kiwon lafiya a nan gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here