Yan ta’adda sun yi garkuwa da shugaban Hukumar tattara arzikin kasa

0
71

Yan bindiga sun yi garkuwa da shugaban Hukumar tarawa da rabon arzikin kasa Alhaji Bashir Abara Gummi, tare da wasu matafiya a kan babbar hanyar Funtua zuwa Gusau dake jihar Zamfara.

Yan ta’addan sun tare babbar hanyar a ranar Lahadi, inda suka sace matafiya da dama, tare da shi.

Karanta karin wasu labaran:Yan ta’adda zasu kaiwa al’ummar Zamfara harin ramuwa

Wasu majiyoyi daga bangaren tsaro sun bayyana cewa a lokacin harin, ’yan ta’adda sun bude wa motocin da ke wucewa wuta, ind suka kashe mutune biyu kafin su sace Alhaji Bashir da sauran matafiyan.

Alhaji Bashir Abara Gummi ya fada hannun ’yan ta’addan ne a lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa Abuja aiki, a cewar wani jami’in hukumar.

Sai dai Babban Mai Binciken Kudi na Jihar Zamfara, Alhaji Abubakar Dan Maliki, ya tsallake rijiya da baya, sakamakon samun damar tserewa a lokacin harin.

Rahotanni sun nuna cewa motarsa ta iso wajen da abin ya faru bayan da ’yan bindiga suka tare rukunin farko na motoci, amma ya yi sauri ya juyar da motar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here