Gwamnan Kano ya mikawa Sarkin Gaya Sandar Mulki

0
150

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bawa Sarkin Gaya da aka sake nadawa, Alhaji Aliyu Ibrahim Abdulkadir, sandar mulki.

A yanzu, sarkin yana da matsayin sarki mai daraja ta biyu, bayan gyara dokar masarautun Kano da majalisar dokokin jihar tayi.

Idan za’a tuna an sake nada Sarki Abdulkadir ne bayan sake nada Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, bayan cire Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero.

Karanta karin wasu labaran:Asibitin Aminu Kano ya kula da wadanda suka kone a Jigawa ba tare da kudin magani ba

Sarki Abdulkadir ya amince da sauke shi da Gwamnatin Kano ta yi bayan soke dokar masarautun jihar da Majalisar Dokoki ta Jihar Kano ta yi, amma daga baya gwamnan ya sake nada shi.

A yayin mika sandar mulkin, Gwamna Abba ya nemi sarkin ya zama abin koyi kuma ya jagoranci wadanda suke karkashin sa yadda ya kamata, cikin gaskiya da rikon Amana.

Ya kuma bayyana rawar da sarakunan gargajiya ke takawa wajen tabbatar da zaman lafiya da ci gaban al’ummarsu.

Sarkin Gaya, Alhaji Aliyu Ibrahim Abdulkadir, ya gaji mahaifinsa, Ibrahim Abdulkadir, wanda ya rasu a ranar 22 ga watan Satumba 2023, yana da shekara 91.

Tsohon Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, ne ya fara nada shi Sarkin na Gaya.

Taron mika sandar ya samu halartar sarakunan Kano, Rano, Karaye, da sauran manyan baki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here